24 Afirilu 2018 - 12:49
AN GUDANAR DA JANA'IZAR SHADIN ABUJA SHAHID AHMAD RUFA'I A YAU TALATA A JANNATU DARURAHAMA

A safiyar yau talata 24/04/2018 ne aka gudanar da Jana'izar Shidin Abuja wato Shahid Ahmad Rufa'i a Darur Rahama dake dambo a garin Zaria, Shahid Ahmad Rufa'i yayi shahada ne sakamakon harbin da yan sandan Nigeria suka masa a garin Abuja wajen Muzaharar Neman a saki Jagoran Harkar Musulunci a Nigeria wato Sayyid Zakzaky {H} An harbe shine a kansa a ranar litini 16/04/2018, ranar alhamis kuma Allah ya amsa abinsa, a safiyar yau talata kuma aka rufe sa a makwancin shahidai wato Darur Rahama, bayan an rufe shine Sheikh Abdulhamid Bello ya tunatar da yan uwa, matsayin shahada da kuma darajar shahidai , yayi kira kuma ga yan uwa da su dake a wannan Harkar kamar yanda Shahidan mu suka dake har suka samu rabo. bayan ya kammala ne akayi addu'oi aka sallami Mutane

shahid

shahid

shahid

shahid